MACE SAI DA GYARA: Abubuwa 12 Wadanda Duk Matar Da Ta Rike Su Za Ta Samu Alkhairi A Rayuwarta Ta aure


    
1 – Ki Zama Kamar Baiwa Ga Mijinki, Sai Shi
Ma Ya Zama Kamar Bawa A Gare Ki.

1 – Kada Ki Nisance Shi; Sai Ya Manta Da ke.

3 – Ki Kiyaye Masa Hancinsa, Jinsa, Da
Ganinsa; Kada Ya Shaqi Wani Abu Daga Gare
Ki Sai Mai Kamshi, Kada Ya Ji Wani Abu Daga
Bakinki Sai Mai Dadi, Kada Ya Ga Wani Abu
Daga Gare Ki Sai Mai Kyau.

4 – Ki Kiyaye Masa Lokacin Abincinsa Da
Lokacin Baccinsa, Domin Yunwa Tana
Hassala Mutum, Kuma Ta Gurbata Masa Bacci
Ta Fusata Shi.

5 – Ki Kiyaye Masa Dukiyarsa, Danginsa Da
Gidansa, Domin Suna Da Matukar
Muhimmanci A Gare Shi.

6 – Ki Guji Yin Farin Ciki Yayin Da Yake Cikin
Bacin Rai, Kuma Ki Kiyayi Yin Bakin Ciki, Yayin
Da Yake Farin Ciki.

7 – Ki Girmama Shi Matuka; Shi Ma Zai
Girmamaki Matuka Fiye Da Yadda Kowa Zai
Girmamaki.

8 – Ki Sani Cewa Gwargwadon Yadda Kike
Amincewa Da Ra’ayinsa Gwargwadon
Tausayawar Da Zai Miki.

9 – Kada Ki Juya Masa Baya Yayin Da Ya
Kusanto Gare Ki.

10 – Ki Sani Baza Ki Sami Yadda Kike So Ba
Har Sai Kin Zabi Yardarsa Akan Yardarki, Kin
Fifita Son Ransa Akan Son Ranki.

11 – Kada Ki Fiya Naci Ko Fushi A Lokacin Da
Kike Neman Wani Abu A Gare Shi, Sai Ya Kosa
Dake.

12 – Daga Karshe Don Girman ALLAH Ki Yi
Hakuri, Ki Zamo Shimfida Ga Mijinki Zai Zamo
Rumfa A Gare Ki.