Advertisement

Babbar Magana: Tun da aka haifeni babu wani saurayi da ya taba zuwa yace yana sona – Budurwa

Babbar Magana: Tun da aka haifeni babu wani saurayi da ya taba zuwa yace yana sona – Budurwa
Babbar Magana: Tun da aka haifeni babu wani saurayi da ya taba zuwa yace yana sona – Budurwa

A wani labari da jaridar ireporteronline ta wallafa a shafinta, ta bayyana yadda wata budurwa ke shirin daukar ranta saboda tsabar bakin ciki.

Duk da dai jaridar bata bayyana ainahin sunan budurwar ko kuma garin da ta fito ba, amma jaridar ta wallafa hoton budurwar da kuma irin halin da ta shiga saboda rashin masoyi, wanda har ya kai ga ta fara neman kashe kanta saboda bacin rai.

Ga dai abinda budurwar ta rubuta a kasa:

“Shekaruna 22 kuma babu wani saurayi da ya taba zuwa wajena. Anti na da ta kawo mini ziyara ta bukaci na fara soyayya, tunda ban taba yin saurayi ba.

“Ta tambayeni ko akwai wanda ya taba cewa zai fita yawo dani, nace mata babu wani namiji da ya taba zuwa kusa dani, sai abin ya bata mamaki sosai.

Kwarai kuwa nima na kasa gane a ina matsalar take?

“Ban tunanin ina da munin da mutane zasu dinga guduna, Ina da tsawo daidai gwargwado, jikina daidai misali. Lokuta da dama ina mutane na yawan yin magan game da yanayin kyawun jikina.

“Amma idan ‘yan uwana suka tambayeni shin ina da saurayi, amsar dana ke basu na basu mamaki sosai, da yawa daga cikinsu na kwantar mini da hankali suce zan samu saurayi, saboda yanayin dirina, amma ban san wane dalili ne ya sanya har yanzu ban samu ba.

“Na gaji da rayuwar nan, ina so komai ya zo karshe, ji nake tamkar na kashe kaina na huta da wannan bakin cikin.

To ance dai komai yayi zafi maganinsa Allah, muna addu’ar Allah ya fito mata da masoyi, ya kuma nesanta ta daga aikin dana sani. Amin.

Drop Your Comment

0 Comments